Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Maki shida ne tsakanin Madrid da Barcelona a La liga

Tazarar Maki shida ne yanzu tsakain Real Madrid da Barcelona, bayan a daren jiya Real Madrid ta sake yin kunnen doki ci 1-1 da Villareal. Cristiano Ronaldo ne ya zirawa Madrid kwallo a raga, kwallon shi ta 33 a La liga.

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo a lokacin wasan da suka yi kunnen doki ci 1-1 da Villareal
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo a lokacin wasan da suka yi kunnen doki ci 1-1 da Villareal REUTERS/Heino Kalis
Talla

Amma saura minti Takwas a kammala wasan ne Marcos Senna ya barke wa Villareal kwallonta.

Sai dai alkalin wasa ya rage yawan ‘yan wasan Madrid zuwa ‘Yan wasa Tara bayan daga jan kati ga Sergio Ramos da Mesut Ozil tare da sargahe Mourinho a wajen ‘yan kallo.

A ranar Talata Barcelona ta doke Granada ci 5-3 wasan da Messi ya kafa tarihin wanda ya fi kowa zira kwallaye a raga a Barcelona.

Bayan kammala wasan Madrid, Ronaldo yace fashi ne aka yi masu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.