Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Barcelona da Madrid sun haska, PSG tasha kashi a Faransa

A La liga a Spain har yanzu maki shida ne tsakanin Barcelona da Real Madrid, domin dukkaninsu sun lashe wasanninsu a karshen mako. A Faransa PSG ta sha kashi hannun Nancy, wasan farko da aka samu galabar Carlo Ancelotti.

Kocin PSG Carlo Ancelotti.
Kocin PSG Carlo Ancelotti. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Barcelona ta doke Athletic Bilbao ci 2-0, Messi ne da Andres Iniester suka zirawa Barcelona kwallayenta a raga.

Real Madrid kuma ta lallasa Osasuna ci 5-1, kwallayen da Ronaldo da Higuin da Benzema suka zira wa Madrid.

Italiya

A Italia kuma yanzu maki biyu ne Milan taba Juventsus a Tebur na Seria A, domin Juventus ta doke Napoli ci 3-0. Milan kuma ta yi kunnen doki ne ci 1-1 da Catania.

Sabon Kocin Inter Milan, Andrea Stramaccioni ya samu nasarar lashe wasan shi ta farko a matsayin kocin Inter. Bayan Inter ta doke Genoa ci 5-4.

Faransa

Lille ta fara samun kwarin gwiwar lashe kofin French League, bayan ta doke Toulouse ci 2-1. Kuma yanzu maki 4 ne tsakaninta da Montpellier dake jagorancin Tabur

A karshen mako kuma Carlo Ancelotti ya sha kashi hannun Nancy ci 2-1, a wasan farko da aka samu galabar shi tun fara aikin horar da ‘yan wasan PSG.

Sai dai an dage wasa tsakanin Montpellier da Marseille zuwa 11 ga watan Aprilu, domin ba Marseille damar shirya wasanta da Bayern Munich a gasar Zakarun Turai.

Jamus

A Bundeliga ta kasar Jamus Bayern Munich ta doke Nuremberg ci 1-0, kuma yaznu maki uku ne tsakaninta da Dortmund bayan an tashi wasan da Dortmund ta buga da Stuttgart ci 4-4.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne za’a yi karon batta inda Dortmund zata karbi bakuncin Bayern Munich.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.