Isa ga babban shafi
Wasanni

Shiri akan Matashin dan wasa mai kishin bugawa Najeriya kwallo

Wallafawa ranar:

A cikin shirin zaku ji wani matashin dan wasan kwallon kafa a arewacin Najeriya wanda gurinsa shi ne bugawa kasarsa Najeriya kwallo, kuma matashin da mahaifin shi ke taimaka masa domin cim ma wannan gurin na shi.  

Rigar kwallon kafar 'Yan wasan Najeriya
Rigar kwallon kafar 'Yan wasan Najeriya bbk Shirt
Talla

Wasan kwallon kafa dai yanzu shi ne wasan da ya dauki hankilin duniya, kusan yanzu wasan kwallo kafa ta mamaye duniya baki daya inda ake gudanar da wasan iri daya ba tare wani banbanci ba.

Kuma saboda mamaye duniya da kwallon kafa ta yi kasashen duniya ke haduwa a kasa daya domin gudanar da gasar cin kofin Duniya.

Najeriya dai na daya dga cikin kasashen a Nahiyar Afrika da ta yi fice a kwallon kafa, kuma akwai ‘yan Najeriya da dama a kasashen duniya da ke taka kwallo yanzu haka. Shirin duniyar wasannin ya zanta ne da Muhammad Najib Nuradeen, wani matashin dan wasan kwallon kafa a unguwar lowcoast Binji Phamacy Sokoto wanda sananne kuma kwararren dan wasan kwallon kafa a jihar.

Muhammad Najib ya fara kwallon kafa tun yana yaro kafin kuma ya ci gaba da samun horo a wata makarar kwallon kafa ta tsohon dan wasan Super Eagle Tijjani Babangida a Sokoto, kuma Najib ya taba samun horo a wata makarartar tsohon kocin Super Eagle Samson Siasia a Abuja.

Muhammd Najib ya shaidawa shirin Duniyar Wasanni cewa Yanada kudurin wakiltar Najeriya nan gaba a wasan kwallon kafa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.