Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Zakarun Turai: Za’a fitar da gwani tsakanin Milan da Barcelona

A yau Talata ne Barcelona zata karbi bakuncin AC Milan a filin wasa na Nou Camp. A karawar farko AC Milan ta harmatawa Barcelona zira kwallo a ragarta inda aka tashi wasan babu ci.

Tambarin Barcelona da AC Milan a karawar da zasu yi a gasar zakarun Turai
Tambarin Barcelona da AC Milan a karawar da zasu yi a gasar zakarun Turai
Talla

Sai dai a yau ba’a san yadda wasan zata kaya ba a Nou Camp, amma ana iya cewa Barcelona tana da kwarin gwiwa domin a gidanta ne za’a buga wasan, kuma ko a haduwarsu a zagayen farko Barcelona ta lallasa AC Milan.

Pedro matashin dan wasan Barcelona yace wannan wasa da Milan wasa ne mafi muhimmci ga Barcelona a bana domin gurin su shi ne tsallakawa zagayen kusa da karshe.

A yau ana tunanin Fabregas zai haska a wasan bayan murmujewa daga raunin da yaji a kafadar shi.

Sai dai ana hasashen za’a buga wasan ba tare da Xavi Hernandez ba, Domin Guardiola yace kwana biyu dan wasan bai samu fitowa horo ba saboda rauni a kafar shi.

A yau ne kuma Bayern Munich ta kasar Jamus zata karbi bakuncin Olympique Marseille bayan lallasa Olympique Marseille a gidanta ci 2-0.

Dan wasan Bayern Munich Bastian Schweinsteiger wanda zai kauracewa wasan saboda ba shi jan kati ya bukaci abokan wasan shi lallasa Marseille.

Wannan kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da Aryen Robben dan wasan Bayern Munich zai tsawaita kwangilar shi da kungiyar har zuwa shekarar 2015.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.