Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Madrid zata kara da APOEL, Benfica zata kece raini da Chelsea

A yau Laraba ne Real Madrid zata karbi bakuncin APOEL Nicosia ta Cyprus a Filin wasa na Santiago Bernabeu, Kungiyar Benfica kuma zata nemi rama kwallon da Chelsea ta zira a ragarta a Stamford Bridge.

Dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic  a lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Aston Villa a gasar Premier ta Ingila
Dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic a lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Aston Villa a gasar Premier ta Ingila REUTERS/Toby Melville
Talla

Kocin Madrid, Jose Mourinho yace babu wani sauyin ‘Yan wasa da zai yi a wasan wai don Madrid tana da kwallaye uku a ragar APOEL.

A karshen mako ne Real Madrid zata kace raini da Valencia a Bernabeu kuma ana hasashen Mourinho zai iya ajiye zaratan ‘Yan wasan shi don gudun kada ya barar da maki saboda hamayyar shi da Barcelona a La liga.

Mourinho yace APOEL tana iya zira kwallaye hudu a ragar Madrid don haka ya zama dole Madrid ta iyar da aikinta.

Idan dai Madrid ta tsallake zagayen kusa da karshe zata kara ne Bayern Munich.
A yau ne kuma Kungiyar Chelsea tilo daga Ingila zata kara da Benfica a Stamford Bridge.

A wasan farko Chelsea ta zira kwallo daya mai ban haushi a ragar Benfica.

Amma kocin Benfica Jorge Jesus yace kwallon da Chelsea ta zira a raga sa’a ce, domin yace ya yi imanin zasu lallasa ‘Yan wasan “The Blues” a yau Laraba.

Amma kocin Chelsea Di Matteo ya bukaci ‘yan wasan shi buga kwallo kamar yadda suka yi waje da Napoli ta kasar Italia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.