Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Real Madrid ta sha kashi hannun Bayern Munich

Real Madrid tasha kashi hannun Bayern Munich ci 2-1. A wasan farko a zagayen kusa da karshe A gasar zakarun Turai. Amma Mourinho kocin Madrid yace yana da kwarin gwiwar buga wasan karshe a filin wasa na Allianz Arena a watan Mayu.

Kocin Real Madrid Jose Mourinho
Kocin Real Madrid Jose Mourinho Reuters
Talla

Ana gab da kammala wasan ne Mrio Gomez ya zira kwallo ta biyu a ragar Real Madrid bayan Franck Ribery ya zira kwallo ta farko mintina 17 da fara wasa.

Mesut Ozil ne ya barke kwallon Rivery bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Mourinho kocin Real Madrid yace yana da kwarin gwiwar dawowa filin wasa na Allianz Arena domin buga wasan karshe bayan ya sha kashi a karon farko tun fara gasar zakarun Turai a bana.

A makon gobe ne ranar laraba Real Madrid zata karbi bakuncin Bayern Munich a filin wasa na Bernabeu.

A yau Laraba ne Chelsea zata karbi bakuncin Barcelona a Stamford Bridge, kuma Franck Lampard yace idan suka doke Barcelona zai kasance lokaci mafi tarihi a rayuwar shi.

Chelsea dai zata nemi rama kashin da tasha hannun Barcelona a dai dai irin wannan lokaci shekaru uku da suka gabata.

Lampard ya dade yana haskawa a wasan da Chelsea ke bugawa da manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai, amma dan wasan yace samun galabar Barcelona a wannan lokacin ba karamar nasara bace.

A karshen mako dai Chelsea ta lallasa Tottenham wanda ya bata damar tsallakewa buga wasan karshe da Liverpool a gasar FA, amma Lampard yace nasarar Chelsea akan Tottenham ba zai zama gargadi ga Barcelona ba saboda suna da jerin zaratan ‘Yan wasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.