Isa ga babban shafi
La liga

Clasico: Barcelona da Madrid, Mourinho da Guardiola, Messi da Ronaldo

A gobe Assabar kungiyoyi biyu masu hamayya da Juna, Real Mdrid da Barcelona zasu kece raini a La liga bayan sun sha kashi a gasar zakarun Turai. Amma Messi da Ronaldo zasu haska wadanda suka zira kwallaye 41 a raga a bana.

Josep Guardiola na Barcelona da  José Mourinho na Real Madrid.
Josep Guardiola na Barcelona da José Mourinho na Real Madrid. Reuters
Talla

Maki hudu ne Real Madrid ta ba Barcelona a Tebur, amma Barcelona zata nemi datse yawan makin zuwa daya idan ta samu galabar Madrid a Nou Camp. Madrid kuma zata yi kokarin karbe kofin La liga hannun Barcelona a bana.

Wasa Biyar ne ya rage a kammala La liga.

A bana, Cristiano ya zira kwallaye 53 a raga amma 41 a La liga, Messi Gwarzon dan wasan Duniya sau uku jere wanda ya karbe kyautar hannun Cristiano Ronaldo ya zira kwallaye 63 amma 41 a La liga.

A gobe idan kungiyoyin biyu sun fafata a Clasico, akwai yiyuwar zasu sake haduwa a wasan karshe a gasar Zakarun Turai inda Real zata nemi lashe kofin gasar sau 10, amma Barcelona ce ta lashe kofin a bara kuma take neman lashe kofin sau Biyar.

Sai dai kungiyoyin biyu sun fuskanci barazana a wasansu na farko da suka buga a gasar Zakarun Turai domin Real tasha kashi hannun Bayern Munich ci 2-1, Chelsea kuma ta samu galabar Barcelona ci 1-0.

Shekaru uku da suka gabata Barcelona ta lallasa Real Madrid, kuma a bana Barcelona ta doke Real Madrid a gasar Kings Cup da Super Cup tare da sake lallasa Madrid ci 3-1 a Bernabeu a La liga.

Yana da wahala dai a kammala wasan Clasico ba tare da zargin alkalan wasa wajen taimaka wa Barcelona ba.

Sakamakon wasan clasico a gobe zai iya kasancewa ma’aunin wasannin kungiyoyin biyu a La liga.

Tarihin Hamayyar Clasico

A zamanin nan akwai sabuwar hamayya da aka samu a wasan Clasico tsakanin Ronaldo da Messi wadanda ake ganin tarihin kwallon kafa ba zai taba mantawa da su ba.

Wasan Clasico ta shafi hammaya tsakanin manyan Biranen kasar Spain, Madrid da Barcelona inda Barcelona ke ganin kanta a matsayin mai wakilatar al’ummar yankin Catalonia, Real Madrid kuma ke daukar kanta a matsayin mai wakiltan al’ummar Spaniya. Akwai kuma tasirin Siyasa da ke kara hura wutar hamayya tsakanin kungiyoyin biyu.

Akwai hammayar Clasico tsakanin kafafen yada labaran Spain, inda ko wace kungiya tana da Jaridar da ke mara mata baya tare da yayata nasarorin kungiyar.

Akwai Sabuwar hamayya a Wasan Clasico tsakanin Mourinho da Guardiola, domin Mourinho ya taba zama mataimakin kocin Barcelona lokacin da Guardiola yana dan wasa a shekarar 1990.

Tun fara aikin shi a matsayin kocin Madrid, Mourinho ya sha zargin alkalan wasa wajen nuna goyon bayansu ga Barcelona.

A bara Barcelona ta fitar da Real Madrid a zagayen kusa da karshe a gasar zakarun Turai, bayan lallasa Mourinho ci 5-0 a wasan Clasico na Farko tsakanin shi da Guardiola.

Tsakaninsu kowace kungiya ta lashe wasan gobe zai kasance sun samu nasara 87 da juna a haduwa 219. Tare da yin kunnen doki 46.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.