Isa ga babban shafi
Wasanni

Bayern Munich ta ce tana da jan aiki ranar laraba mai zuwa

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar Jamus Karl-Heinz Rummenigge yace, yana ganin wasan kusa da na karshe karo na 2, da kungiyar shi za ta buga a gasar Champions League, da Real Madrid a ranar laraba mai zuwa, zai yi zafi.A ranar talata da ta wuce Bayernta sha da kyar a zagaye na farko na wasan, yayin da ta yi wa Real din ci 2 da 1 a birnin Munich bayan da da wasan ta na gaba Mario Gomez ya zura kwallon ta, ta 2 a ragar Real din yayin da ake daidai minti 90 da wasan, kuma yanzu za ta je Madrid don haka shugabanta yake ganin suna da jan aiki a gaban su.Ya ce suna sane da cewa akwai zaratan ‘yan wasa a real. 

'Yan wasan Bayern Munich, suna da jan aiki ranar Laraba mai zuwa.
'Yan wasan Bayern Munich, suna da jan aiki ranar Laraba mai zuwa. Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.