Real Madrid ta lashe kofin La liga na 32
Real Madrid ta lashe kofin La liga na 32 bayan ta lallasa Athletic Bilbao ci 3-0. Wannan ne kuma ya kawo karshen zamanin Barcelona wacce ta haramtawa Real Madrid kofin shekaru uku da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Gonzalo Higuain da Mesut Ozil da Cristiano Ronaldo ne suka zira wa Real Madrid kwallayenta a ragar Athletic Bilbao.
Hakan ne kuma yaba mourinho nasarar lashe kofi hudu a kasashe hudu daban daban. Amma Wannan ne kofin La liga na farko da Mourinho ya lashe a Real Madrid.
A jiya dai Dole sai Real Madrid ta doke Bilbao kafin ya lashe kofin domin Barcelona ta lallasa Malaga ci 4-1.
Bayan kammala wasan dai Mourinho ya kauracewa manema labarai, amma ‘Yan wasan shi Iker Casillas da Sergio Ramos dukkaninsu sun bayyana farin cikinsu
Yanzu haka buki ya barke a Madrid tsakanin magoya bayan kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu