Isa ga babban shafi
La liga

Guardiola yace zai yi bankwana da Barcelona a karshen kakar wasan bana

Kocin Barcelona Pep Guardiola, ya shaida wa ‘Yan wasan shi zai yi bankwana da aikin horar da su a karshen kakar wasa, bayan ya shiga kundin tarihin masu horar da ‘Yan wasan Barcelona da suka samu nasarori a kungiyar.

Guardiola Kocin Barcelona a lokacin da ya karbi kyautar gwarzon kocin Duniya
Guardiola Kocin Barcelona a lokacin da ya karbi kyautar gwarzon kocin Duniya REUTERS/Christian Hartmann
Talla

“Yara, zan fice Barca” inji Guardiola a lokacin da ya ke shaidawa ‘Yan wasan shi kamar yadda jaridar Daily Marca ta yada a shafinta na Intanet ba tare da bayyana tushen labarin ba.

Idan an jima ne ake sa ran Guardiola zai gana da manema labarai game da makomar shi bayan ya gana da shugabannin Barcelona da ‘Yan wasan shi.

Guardiola ya kwashe tsawon rayuwar shi a Barcelona, kuma ya taba zama kocin karamar Kungiyar Barcelona ta B kafin ya fara aikin horar da babbar kungiyar a shekarar 2008 inda ya gaji dan kasar Holland Frank Rijkaard.

Shekaru Hudu Guardiola ya kwashe a Barcelona amma ya lashe kofuna 13 tare da tsakulo ‘Yan wasa daga makarantar Barcelona da suka yi fice a fagen Tamola.

Labarin ficewar Guardiola shi ne ya mamaye kanun labaran Jaridun kasar spain.

Da misalin karfe 10:30 Agogon GMT na Safe ake sa ran Guardiola zai gana da manema Labarai.

A ranar Talata ne Chelsea ta fitar da Barcelona a gasar Zakarun Turai bayan Barcelona ta sha kashi a wasan Clasico tsakaninta da Real Madrid.

Kafofin yada Labaran kasar Spain sun ruwaito Barcelona ta fara tunanin masu horar da ‘Yan wasan da zasu gaji Guardiola da suka hada da Kocin Faransa Laurent Blanc, da kocin Olympiakos Ernesto Valverde ko kuma kocin kungiyar Athletic Bilbao ko kocin kasar Argentina Bielsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.