Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Messi ya yi bari, ‘Yan wasan Chelsea 10 sun yi waje da Barcelona

Lionel Messi ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida da yasa Chelsea ta fitar da Barcelona a gasar zakarun Turai bayan ta doke Barcelona a Stamford Bridge ci 1-0 sannan aka tashi wasa ci 2-2 a Nou Camp.

Dan wasan Chelsea Didier Drogba yana ganawa da dan wasan Barcelona Lionel Messi  bayan kammala zagayen kusa karshe a gasar zakarun Turai a Nou Camp
Dan wasan Chelsea Didier Drogba yana ganawa da dan wasan Barcelona Lionel Messi bayan kammala zagayen kusa karshe a gasar zakarun Turai a Nou Camp REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

A karawar Farko a Stamford Bridge Chelsea ta samu galabar Barcelona ci 1-0, kuma a Nou Camp Chelsea ta rama kwallaye 2 da Barcelona ta zira a ragarta bayan alkalin wasa ya ba John Terry Jan kati.

Sergio Busquets ne ya fara zira wa Barcelona kwallonta a ragar Chelsea kafin Andres Iniesta ya sake zira kwallo ta biyu.

Ana mintinan karshe aje hutun rabin lokaci Ramires ya zira kwallo a ragar Barcelona, Fernando Torres kuma ya sake zira kwallo ta biyu bayan ya yanke mai tsaron gidan Barcelona Victor Valdes ana Mintinan karshe a kammala wasan.

Bayan kammala wasan, Kocin Chelsea Roberto Di Matteo ya jinjina wa ‘Yan wasan shi a kokari da kwazon da suka yi na tsallakewa zuwa wasan karshe a Munich.

“Mutane da dama sun yi tunanin zamu fadi amma ‘Yan wasana sun nuna wa duniya kokarinsu” inji Di Matteo.

Pep Guardiola Kocin Barcelona, yace ‘Yan wasan shi sun yi iya kokarinsu domin tsallakewa wasan karshe amma yanzu sai dai hakuri.

A wasan dai Chelsea ta yi amfani da salon tsare gida ne kamar yadda ta yi a Stamford Bridge da ya bata nasara ci 1-0. Barcelona kuma ta fito domin farautar zira kwallo a raga.

Chelsea zata buga wasan karshe tsakanin Real Madrid da Bayern Munich wadanda zasu kece raini a yau Laraba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.