Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Dortmund ta lashe Bundesliga, Madrid ta samu galabar Barcelona a Nou Camp

Borussia Dortmund ta lashe kofin Bundesliga a kasar Jamus. A Spain, Real Madrid ta doke Barcelona a gidanta. A Ingila yanzu maki uku ne Manchester united taba City. Van Persie kuma ya lashe kyatar gwarzon dan wasa. A Faransa, har yanzu maki biyu ne tsakanin Montpellier da PSG.

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo a lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Barcelona a Nou Camp
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo a lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Barcelona a Nou Camp REUTERS/Sergio Carmona
Talla

A karshen mako ne Borussia Dortmund ta lashe kofin Bundesliga bayan taba Bayern Munich tazarar maki 8, ana saura wasanni biyu a karkare gasar.

Sai dai, sai a wasan karshe ne za’a mikawa Borussia Dortmund kofinta a wasansu da Freiburg a ranar 5 ga watan Mayu.

Tun fara bundesliga a bana sau uku ne kacal aka samu galabar Borussia Dortmund. Amma sau hudu ne Borussia Dortmund ke doke Bayern Munich gida da waje domin tun a watan Fabrairun shekarar 2010 Bayern bata samu nasara akan Borussia Dortmund ba.

Sai dai Bayern zata iya rama kashin da tasha a haduwarsu wasan karshe na lashe kofin Jamus da za’a gudanar a ranar 12 ga watan Mayu a birnin Barlin.

Spain

A La liga, Cristiano Ronaldo ya zira kwallon shi ta 54 a raga bana a dai dai lokacin da Real Madrid ke neman lashe kofin La liga na 32 bayan doke Barcelona ci 2-1 a Nou Camp.

Wasanni hudu ne suka rage a kammala La liga, amma bayan doke Barcelona, a shafin zumunta na Twitter Cristiano Ronaldo ya yada cewa “gurinsu ya cika”.

Wannan ne karo na farko da Mourinho ya smau galabar Barcelona a Nou Camp. Kuma yanzu Real Madrid ita ce kungiyar da tafi yawan zira kwallaye a raga a bana bayan zira kwallaye 109.

Bayan kammala Clasico, Guardiola ya amsa shan kashi tare da taya Real Madrid murna.

Ingila

A Premier League dan wasan Arsenal Robin Van Persie aka zaba gwarzon dan wasa bayan ya zira kwallaye 27 a raga.

Van Persie ya doke ‘yan wasan Manchester City guda uku Sergio Aguero, David Silva da Joe Hart, da dan wasan Tottenham Scott Parker da dan wasan Manchester United Wayne Rooney.

A Premier league, Manchester United ta barar da maki biyu a karshen mako bayan an tashi wasa ci 4-4 tsakaninta da Evaton a old Trafford. Manchester City kuma ta samu nasarar lallasa Wolves ci 2-0.

Sakamakon wasan karshen mako nan bai yi wa Ferguson dadi ba domin a mako mai zuwa ne zai yi karon batta da Mancini. Manchester city zata iya darewa saman Tebur da yawan kwallaye idan ta samu galabar United, Inda zai rage saura wasanni biyu a kammala Premier.

Italia

A Seria A, Maki uku ne Juventus taba AC Milan a Tebur, amma kocin AC yace zasu yi kokarin haramta wa Juventus kofin da take kokarin lashewa na farko tun shekarar 2003.

A karshen mako Juventus ta lallasa Roma ci 4-0, wasa na shida da Juve ta buga ba’a samu galabarta ba.

Faransa

A Faransa, yanzu maki biyu ne Montpellier taba PSG a Tebur bayan dukkanin kungiyoyin biyu sun samu nasarar lashe wasanninsu a karshen mako

Montpellier ta samu nasarar doke Valenciennes ci daya mai ban haushi.

Lille da ke rike da kofin yanzu maki biyu ne tsakaninta da PSG bayan ta lallasa Dijon ci 2-0. Wanda zai bata nasarar tsallakawa buga gasar zakarun Turai a badi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.