Isa ga babban shafi
Euro 2012

Jamus ta lallasa Holland, Portugal ta samu sa’ar Denmark

Holland ta sha kashi hannun Jamus ci 2-1 bayan ta sha kashi hannun Denmark a gasar cin kofin Turai da ake gudanarwa a kasashen Ukraine da Poland. Portugal ta samu nasarar doke Denmark ci 3-2.

Hoton Mario Gomez,  da aka hada tare da 'yan wasan Holland  Mark van Bommel  Arjen Robben a lokacin da Jamus ta lallasa Holland ci 2-1 a gasar Turai
Hoton Mario Gomez, da aka hada tare da 'yan wasan Holland Mark van Bommel Arjen Robben a lokacin da Jamus ta lallasa Holland ci 2-1 a gasar Turai Reuters Montage/RFI
Talla

Mario Gomez ne dai ya zira wa Jamus kwallayenta biyu a ragar Holland.

Yanzu haka Holland ita ce kasan Teburin rukunin B, kuma sai ta doke Portugal zata iya samun nasarar tsallakewa zagayen Quarter Final.

A daya bangaren kuma Silvestre Varela ne ya taimaka wa Portugal doke Denmark ci 3-2.

Kasar Jamus ce ke jagorancin Teburin Rukunin B da maki Shida, Denmark kuma da Portugal dukkaninsu suna da maki 3.

A gasar Euro har yanzu Cristiano Ronaldo na Real Madrid bai zira kwallo a raga ba, al’amarin da yasa ‘Yan kallo a wasan Portugal da Denmark suka kama yayata Messi! Messi! abokin adawar Ronaldo a La Liga

A tarihin gasar Turai dai sau Biyar ne Ronaldo ya zira kwallaye a raga a wasannin 15 daya buga tun fara haskawa a gasar a shekarar 2004.

Wasu dai suna ganin kalubalen da Messi ya fuskanta a lokacin gasar cin kofin Duniya shi ne yanzu ya shafi Ronaldo a gasar Turai.

Kocin Portugal Paulo Bento ya kare dan wasan shi inda yace shi ya gamsu da rawar da Ronaldo yake takawa a filin wasa.

Kamar yadda shi kan shi Ronaldo ya mayar da Martani inda yace ko mutane sun san irin rawar da Messi ya taka a bara a gasar Copa Amerika? domin a zagayen quarter Final ne Messi ya fice gasar.

Messi da Ronaldo dai su ne ‘Yan wasa da ke sahun gaba a Duniya da a bana cikinsu ne za’a zabi gwarzon dan wasan duniya.

A yau Alhamis ne Spain mai rike da kofin Turai zata kara da Jamhuriyyar Ireland, daga bisani kuma Italia ta kece raini da Croatia.

Croatia ce dai ke jagorancin Rukuninsu C da maki Uku, sai Spain da Italia masu maki guda. Jamhuriyyar Iraland ce a matsayi na karshe domin a wasan farko tasha kashi hannun Croatia ci 3-1.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.