Isa ga babban shafi
africa

Pistoriuos zai halarci gasar Olympic

Dan gudun tseren kasar Afrika ta Kudu, Oscar Pistorious zai zamanto dan wasa na farko wanda bashi da kafafuwa da zai yi takara a gasar Olympic.Pistoriuos wanda aka yanke mai kafafunsa biyu tun bai kai shekara da haihuwa ba ya na amfani da kafafuwan karfe. 

Dan tseren kafan kasar Afrika ta Kudu, Oscar Pistoriuos (a gaba) a wata gasar tsere
Dan tseren kafan kasar Afrika ta Kudu, Oscar Pistoriuos (a gaba) a wata gasar tsere CBS NEWS
Talla

Zai kuma yi takara ne a gudun mita 400 da kuma mita 4- 400 na mika ka huta, wato, relay.

An haifi da matsala a kafafuwansa wanda hakan yasa aka yanke su daga gwiwa amma hakan bai hana shi cimma burinsa ba a fagen wasanni bayan ya girma.
A da kwallon zari ruga, wato Rugby yak e bugawa amma bayan ya samu matsala a gwiwarsa sai ya koma fagen tsere.

Shekaru hudu da su ka wuce a ka bashi dama ya yi gasa da sauran mutane masu kafafuwa bayan kotun wasanni ta yanke hukunci cewa kafufunsa na karfe ba za su say a fi sauran mutane gudu ba.

Pistorius, dan shekaru 25,ya taba cin azurfa a tseren 4-400 a gasar shekarar 2011 da aka gudanar a Korea ta Kudu
 

Zai kuma je gasar Olympic ta London ta re da sauran ‘yan wasa 65 daga kasar ta Afrika ta Kudu
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.