Isa ga babban shafi
Olympics

Bolt ya lashe kyautar Zinari a tseren gudun Mita 100

Dan kasar Jamaica Usain Bolt ya sake lashe kyautar Zinari a tseren gudun mita 100 bayan lashe zinarin a birnin Beijing. Bolt ya zo na farko cikin dakikoki 9.63, kasa da lukuttan da ya lashe Zinari a shekarar 2009.

Usain Bolt a lokacin da yake murnar lashe tseren gudun Mita 100 a wasannin Olympics
Usain Bolt a lokacin da yake murnar lashe tseren gudun Mita 100 a wasannin Olympics REUTERS/Paul Hackett
Talla

Abokin gudun shi ne Yohan Blake na Jamaica ya lashe kyautar Azurfa bayan ya zo na biyu. Sai kuma dan kasar Amurka Justin Gatlin, wanda ya lashe kyautar Tagulla.

Tseren gudun ya kwashi yan kallo domin ya kunshi fitattun ‘yan tseren gudun duniya guda hudu wato Usian Bolt da Tyson Gay da Asafa Powell da kuma Yohan Blake.

A jiya lahadi ne kuma dan kasar Kenya Ezekiel Kemboi ya lashe tseren gudun Mita 3000, Dan kasar Faransa Mekhissi-Benabear ne ya lashe kyautar Azurfa bayan ya zo na biyu, sai kuma Abel Kiprop Mutai, ya lashe kyaautar Tagulla a matsayin na uku.

Yanzu haka dai kasar Kenya tana da Lambobin yabo 8.

Akwai kuma ‘Yar kasar Habasha Tiki Gelana wacce ta lashe Zinari a tseren gudu Marathon da aka gudunar a kewayen birnin London

‘Yar kasar Kenya ce Priscah ta karbi kyautar Azurfa, sai kuma Tatyana Petrova ta Rasha ta karbi kyautar Tagulla a matsayin na uku.

A tseren mita 10,000 kuma Mo Farah ne na Birtaniya ya lashe Zinari, wanda ya haramtawa fitatacen dan gudun kasar Habasha Kenenisa Bekele lashe zinarin, amma shi ne ya lashe Tagulla.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.