Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Messi da Ronaldo sun dawo a yayin da za a fara gasar La Liga

A yayin da za a fara sabuwar fafatawa a gasar La Liga juko na 2012/2013 a karshen makon nan, dan wasan Barcelona Lionel Messi da dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo sun dawo fagen wasa.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi yana gaisawa da Cristiano Ronaldo a bukin bada kyautar gwarzon dan wasan Duniya
Dan wasan Barcelona Lionel Messi yana gaisawa da Cristiano Ronaldo a bukin bada kyautar gwarzon dan wasan Duniya
Talla

Ko da yake Messi, wanda a jiya ya ce babu wata adawa tsakanin shi da Ronaldo dan wasan Real Madrid, ya zargi kafofin yada labarai da ruruta wutar nuna cewa akwai wata adawa a tsakaninsu.

Ya kara da cewa kafofin yada labarai ne su ke so su hada su amma shi ana shi bangaren bashi da damuwa da Ronaldo.

‘Yan wasan biyu dai su na kusan kunnen doki ne a mafi yawan lokuta a fagen zira kwallaye a raga, inda Messi ya zira kwallaye 50 kana Ronaldo ya zira kwallaye 46 a kakar wasan da ta wuce.

A gobe Asabar ne dai za a fara gasar ta La Liga inda club din Celtic za ta kara da Malaga, sannan Seville za ta fafata ne da Getafe a yayin da Mallorca za ta kara da Espanyol.

A ranar Lahadi kuwa za a fafata ne tskanin Real Madrid da Valencia kana Athletico Bilbao za ta kece raini da Betis inda a wani bangaren kuma Barcelona za ta kara da Real Socieded. Sannan Athletico Madrid ta kara Levante.

A ranar Litini kuwa za a kara ne tsakanin Deportivo da Osasuna da kuma Rayo da Granada, sannan Zaragoza ta fafata Valladolid.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.