Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Barcelona za ta kara da Celtic, Chelsea da Donetsk, United da Braga

A yau Talata ne Kungiyar Chelsea mai rike da kofin gasar zakarun Turai za ta kai wa Shakhtar Donetsk ziyara a karon farko a kasar Ukraine, Barcelona kuma za ta karbi bakuncin Celtic a Nou Camp, Manchester United kuma ta kece raini da Braga a Old Trafford.

Tambarin gasar Zakarun Turai
Tambarin gasar Zakarun Turai
Talla

Kungiyar Barcelona za ta buga wasan ne ba tare da wasu manyan ‘Yan wasanta ba da ke tsare mata baya, Gerard Pique da Carles Puyol da Dani Alves wadanda dukkaninsu suna jinyar rauni.

A yau ne Bayern Munich za ta nemi huce kashin ta sha hannun Bate a karawarta da Lille ta kasar Faransa.

Wannan ne kuma karon farko da Chelsea za ta kai wa Shakhtar Donetsk ziyara a kasar Ukraine.

A karhsen makon nan Chelsea ta lallasa Tottenham Hotspur ci 4-2 duk da cewa Tottenham din ce ta fara zira kwallaye biyu kafin daga bisani Chelsea ta barke kwallayen.

Wannan ne kuma karon farko da Chelsea ta samu galabar Tottenham tun a watan Ogustan shekarar 2005.

Robin Van Persie yace yana jin dadin wasa da Rooney a matsayin ‘Yantawayen Ferguson a filin wasa. A karshen mako Rooney da Van Persie su ne suka taimakawa United doke Stoke ci 4-2.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.