Kwallon Kafa
Beckham zai yi bankwana da LA Galaxy
Tsohon jagoran Ingila David Beckham yace a watan Gobe ne zai yi bankwana da kungiyar LA Galazy a lokacin da kungiyar zata karbi bakuncin Houston a League din Amurka. A yau ne dai dan wasan ake sa ran zai gana da manema labarai domin bayyana dalilin daukar matakin.
Wallafawa ranar:
Talla
Beckham dai ya kwashe tsawon shekaru Shida a Amurka kungiyar Galaxy. Kuma Beckham ya lashe kofin Premier kusan rabin Dozin a Manchester United da kofin FA guda biyu da gasar Zakarun Turai a shekarar 1999 kafin ya koma Real Madrid inda ya lashe La liga a kakar wasa ta 2006.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu