Amurka
Beckham ya buga wa Galaxy wasan karshe
A karshen mako ne David Bchkham ya buga wa kungiyar LA Galaxy ta kasar Amurka wasan karshe bayan kwashe shekaru 6 yana taka kwallo a Amurka. Dan wasan ya taimakawa kungiyar lashe gasar Major League Soccer karo biyu a jere da jere Bayan sun doke Houston ci 3-1 a wasan karshe.
Wallafawa ranar:
Talla
Yanzu dai Beckham zai koma wata kungiya ce bayan ya samu nasarar lashe kofuna a LA Galaxy da Real Madrid da kuma Manchester United. Ana sa ran Beckham zai bayyana sunan kungiyar da zai koma kafin kammala kakar wasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu