Swansea ta doke Chelsea a Stamford Bridge
Kungiyar Chelsea ta sha kashi hannun Swansea City ci 2-0 a gasar cin kofin kalubalen Ingila da aka gudanar Filin wasa na Stamfrod Bridge zagayen kusa da karshe. Rafael Benetez yace rashin sa’a ne ya sa Chelsea ta sha kashi. Swansea kuma ta samu nasarar jefa kwallayen ne a ragar Chelsea saboda kuskuren kwallo daga Ivanovic.
Wallafawa ranar:
Wannan kofin ne dai Chelsea ta sa ma ranta amma kuma ga kofin yana neman ya kubuce. Wasu Masoya Chelsea dai suna ganin gwara Di Matteo da Benetez.
A ranar Talata ne dai Bradford City daga mataki na hudu a league din Ingila ta lallasa Aston Villa ta Premier League ci 3-1 a karawar farko.
A ranar 23 ga watan Janairu ne dai Chelsea da Aston Villa zasu nemi rama kashin da suka sha, ko kuma su kwashi kunyarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu