Isa ga babban shafi
CAF

Tarihin gasar Cin kofin Afrika

An fara gudanar da Gasar Cin Kofin Afrika ne tsakanin kasashe Uku kafin gasar ta koma tsakanin kasashe 16. Kuma yanzu Gasar takan dauki hankalin Miliyoyin mutanen Afrika masu sha’awar kwallon kafa. Mun yi nazarin gasar tun a shekarar 1957da aka fara gudanarwa a kasar Sudan zuwa shekarar 2012 da aka gudanar a kasashen Gabon da Equatorial Guinea, tare da bayanin yadda kasar Masar ta lashe kofin Gasar sau Bakwai, Kamaru da Ghana kuma suka lashe Kofin gasar Sau Hudu hadi da wasu kasashe 11 da suka samu nasarar lashe kofi.

Tambarin Hukumar CAF da ke kula da Kwallon kafa a Nahiyar Afrika
Tambarin Hukumar CAF da ke kula da Kwallon kafa a Nahiyar Afrika
Talla

1957
A shekarar da aka fara gudanar da gasar, Kasar Afrika ta kudu ta fice wanda ya ba kasar Masar nasarar lashe kofin gasar bayan Diab Al Attar ya zirara kwallaye 4 a ragar Habasha a wasan karshe.

1959
Kasar Masar ce ta sake lashe kofin gasar tsakanin kungiyoyi uku da suka shiga gasar inda Sudan ta sha kashi ci 2-1 a hannun Masar.

1962
A shekarar 1962, kasar Habasha ta samu sa’a akan Masar ci 4-2 a wasan karshe. Hakan ne kuma ya janyo hankalin Tunisia da Uganda su shiga gasar a karon farko.

1963
Kasar Ghana ce ta lashe kofin gasar a karon Farko bayan lallasa Sudan ci 3-0. A lokacin an samu karin kasashe zuwa 6 da suka shiga gasar. Kuma lokacin ne Masar ta lallasa Najeriya ci 6-3.

1965
Kasar Ghana ce ta sake lashe kofin gasar da aka gudanar tsakanin kasashe 6 inda ta lallasa Tunisia ci 3-2.

1968
Kasar Habasha ce ta karbi bakuncin gasar da ta kunshi kasashe 8 da har ya kai aka buga wasan kusa da karshe. A lokacin kasar Jamhuriyyar Congo ce ta lashe kofin gasar bayan doke Ghana ci 1-0.

1970
Kazalika kasar Ghana ce ta buga wasan karshe tsakaninta da Sudan amma Sudan ce ta lashe kofin gasar da ci 1-0.

1972
A shekarar ce kasar Congo Brazzaville ta lashe kofin gasar bayan ta samun sa’ar kasar Mali ci 3-2 a birnin Yawunde na kasar Kamaru.

1974
A karon farko a shekarar 1974 ne aka maimaita wasan karshe tsakanin Congo da Zambia amma kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ce ta lashe kofin gasar da ci 2-0 bayan sake fafatawa a birnin Alkahira.

1976
Kasar Morroco ce ta lashe kofin gasar bayan samun rinjeyen maki fiye da kasar Guinea a gasar da aka gudanar a kasar Habasha.

1978
A shekarar ce kasar Ghana ta lashe kofinta na Uku bayan Opoku Afriyie ya zira kwallaye biyu a ragar Uganda a birnin Accra. a lokacin Najeriya ta samu matsayi na uku bayan Tunisia ta fice a karawar neman na uku.

1980
A karon Farko Najeriya ta samu sa’ar lashe kofin gasar a gida bayan lallasa Algeria ci 3-0.

1982
A shekarar ce kasar Ghana ta lashe kofinta na Hudu bayan doke kasar Libya mai masaukin baki ci 7-6 a bugun daga kai sai mai tsaron gida. A shekarar ce kuma Abedi Pele ya fara haskawa kafin ya zama fitaccen dan wasa a Duniya.

1984
Kasar Kamaru ce ta lashe kofin gasar bayan doke Najeriya ci 3-1.

1986
Kasar Masar ce ta sake lashe kofin gasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida tsakaninta da Kamaru a birnin Alkahira.

1988
Karo na uku da kasar Kamaru ke zuwa zageyn karshe a jere da jere, inda ta sake lashe kofin bayan doke Najeriya.

1990
A shekarar ce Algeria ta lashe kofin bayan doke Najeriya a wasan farko da wasan karshe.

1992
A wannan karon ne gasar ta koma tsakanin kasashe 12, kuma a shekarar ce aka buga wasan karshe tsakanin Cote d’Ivoire da Ghana a Senegal. Kasar Cote d’Ivoire ce ta lashe kofin gasar ci 11-10 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

1994
Najeriya ce ta lashe kofin gasar bayan doke Zambia ci 2-1 bayan hadarin Jirgi ya kashe ‘Yan wasan Zambia a kasar Gabon.

1996
A shekarar ce aka fara gudanar da gasar Tsakanin kasashe 16 inda kasar Afrika ta Kudu ta fara haskawa bayan kwashe shekaru ana gudanar da gasar ba tare da ita ba saboda rikicin cikin gida. Afrika ta Kudu ce dai ta lashe kofin gasar bayan doke Tunisia ci 2-0.

1998
Kasar Afrika ta Kudu ta sake samun kai wa zagayen karshe, amma kasar Masar ce ta lashe kofin gasar a Ouagadougou kasar Burkina Faso.

2000
A Najeriya aka gudanar da gasar kuma kasar Kamaru ce ta samu nasarar lashe kofi bayan doke Najeriya ci 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

2002
Kasar Kamaru ce ta lashe kofin gasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida tsakaninta da Senegal a Bamako.

2004
Kasar Tunisia ce ta lashe kofin gasar bayan doke Morocco ci 2-1.

2006
Kasar Masar ce ta lashe kofin gasar a wasan karshe tsakaninta da Code d’Ivoire.

2008
Kasar Masar ce ta kare kambunta bayan samun nasara a wasan karshe tsakaninta da Kamaru.

2010
A shekarar ce kasar Masar ta lashe kofin gasar sau uku a jere a birnin Luanda bayan doke kasar Ghana.

2012

Kasar Zambia ce ta lashe kofin gasar a birnin Libreville bayan doke Cote d’Ivoire ci 8-7 a bugun daga kai sai mai tsaron gida. A lokacin manyan kasashe da suka yi fice a gasar ba su samu damar tsallakewa ba da suka hada da Masar da Kamaru da Najeriya da Algeria. A Shekarar ce kasar Nijar ta fara haskawa a gasar karon Farko.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.