Isa ga babban shafi
Spain

Real Madrid ta samu ribar Kudi fiye da sauran Kunkiyoyin Turai

A Nahiyar Turai, Kungiyar Real Madrid ta Spain ta kasance kungiya ta farko da ta samu ribar kudi euro Miliyan 500 a Shekara, kamar yadda kamfanin hada hadar kudi na Deloitte ya ruwaito.

Filin wasa na Santiago Bernabeu na Kungiyar Real Madrid a Spain
Filin wasa na Santiago Bernabeu na Kungiyar Real Madrid a Spain REUTERS/Sergio Perez
Talla

Sakamakon wanda shi ne karo 16 da aka fitar, ya nuna Real Madrid ce akan gaba wajen samun riba tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a Turai sai Barcelona da ke bi mata a matsayi na biyu.

Cikin jerin Kungiyoyi 10, Manchester United ce a matsayi nau Uku, sai Bayern Munich, a matsayi na Hudu, sannan Chelsea da Arsenal a matsayi na Biyar da matsayi na Shida. Manchester City ce a matsayi na Bakwai.

Kungiyar AC Milan ce a matsayi na 8 sannan Liverpool a matsayi na 9, Juventus kuma a matsayi na 10.

Sakamakon ya nuna Kungiyar Real Madrid ta samu riba a tsakanin 2011 zuwa 2012 da kashi Bakwai wanda ya tasamma jimillar kudi euro Miliyan 512.6.

Wannan ne kuma karo na Takwas da Real Madrid ke jagorantar Teburin Riba tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a Turai, kamar yadda Manchester United ta jagoranci Teburin daga 1996 zuwa 1997 da kuma 2003 zuwa 2004.

A bara Real Madrid ta lashe kofin La liga bayan kwashe shekaru uku a jere Barcelona tana lashe kofin, amma Bayern Munich ce ta fitar Real Madrid a gasar Zakarun Turai zagayen kusa da karshe.

A daren jiya Laraba Real Madrid ta tsallake zagayen kusa da karshe a gasar Copa Del Ray bayan ta yi kunnen doki da Valencia. Amma a karawar farko Real Madrid ta doke Valencia ne ci 2-0.

A yau Alhamis ne kuma Barcelona za ta sake fafatawa tsakaninta da Malaga bayan sun tashi ci 2-2 a karawar farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.