An tuhumi Pistorius dan tseren gudun guragu da kisan Budurwar shi
‘Yan sandan kasar Afrika ta Kudu sun tuhumi dan tseren gudun guragu da laifin kisan budurwar shi a lokacin bukin ranar masoya da ake kira Valentine. Babban Jami’in ‘Yan sanda, laftanal Kanal Katlego Mogale shi ne ya tabbatar da tuhumar da suke wa dan tseren gudun guragun wanda ya karbi lambobin yabo a wasannin Olympics da aka gudanar a birnin London.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
‘Yan sanda sun ce burdurwar shi ta sha harsashen bindiga ne har sau hudu, wadda kawayenta suka kira da sunan Steenkamp.
Masu gabatar da kara a kasar Afrika ta Kudu sun dage sauraren karar Oscar Pistorius, har sai zuwa ranar Juma’a saboda za su gudanar da gwajin jini.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu