Isa ga babban shafi
Olympics

Usain Bolt ya kafa Tarihi a London bayan kafa tarihin a Beijing

Usian Bolt ya kafa tarihi a wasannin Olympics da ake gudanarwa a London bayan yak are Zinarin da ya lashe a Beijing na tseren gudun Mita 100 da Mita 200. Bolt ya lashe tseren Mita 200 ne cikin dakikoki 19.32.

Dan tseren gudun kasar Jamica Usain Bolt beija yana sunbatar Zinarin da ya lashe a tseren gudun mita 200
Dan tseren gudun kasar Jamica Usain Bolt beija yana sunbatar Zinarin da ya lashe a tseren gudun mita 200 REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Bolt yace abinda ya ke neman ke nan kuma yanzu shi ne zakaran duniya.

Abokin gudun Bolt ne dan kasar Jamica Yohan Blake ya lashe kyautar Azurfa bayan ya zo matsayi na biyu cikin dakikoki 19.44 sai kuma Warren Weir shi ma Dan Jamica wanda ya karbi kyautar Tagulla bayan ya zo matsayi na uku cikin dakikoki 19.84.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.