Owen zai yi bankwana da taka leda
Tsohon dan wasan Ingila Michael Owen yace zai yi bankana da taka leda a ajin kwararru idan an kammala kakar wasan bana. Owen yana da shekaru 33 ne na haihuwa kuma dan wasan ya zira wa Ingila kwallaye 40 a haskawa 89.
Wallafawa ranar:
Michael Owen ya taba lashe gwarzon dan wasan Turai a 2001. Amma daga baya tauraruwar dan wasan ta fara tushewa ne saboda fama da rauni.
Owen yana da shekaru 12 ya fara taka kwallo a Liverpool inda ya kwashe shekaru yana jefa kwallaye a raga.
A bara ne Owen ya koma Stoke City bayan kwashe shekaru uku a Manchester United, Sai dai tun zuwansa Stoke City kwallo guda kacal ne Michael Owen ya zira a raga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu