Manchester City ta doke Manchester United a Old Trafford
Sergio Aguero wanda ya shigo daga baya shi ne ya jefa kwallo ta biyu daya ba Manchester City nasarar doke Manchester United ci 2-1 wanda kuma hakan ya rage yawan makin da United ke jagorancin teburin Premier zuwa maki 12.
Wallafawa ranar:
Duk da samun wannan nasarar amma Kocin Manchester city Roberto Mancini yace kofin ya ma shi nisa, sai dai kuma yace ‘Yan wasan shi sun cancanci lashe wasan.
A daya bangaren kuma Kocin Maanchester United Sir Alex Ferguson yace ba su da sa’a, wanda kuma wannan ne ya kawo karshen haskawar da United ke yi ba tare da samun nasararta ba a wasanni 18 da ta buga
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu