Isa ga babban shafi
Champions League

Dortmund ta sha da kyar, Madrid ta yi waje da Galatasaray

Real Madrid da Borussia Dortmund sun tsallake zuwa zagayen dab dana karshe a gasar Zakarun Turai inda Borussia Dortmund ta sha da kyar a hannun Malaga ci 3-2. Bayan kungiyoyin biyu sun tashi babu ci a karawa ta farko.

Didier Drogba wanda ya jefa kwallo ta biyu a ragar real Madrid
Didier Drogba wanda ya jefa kwallo ta biyu a ragar real Madrid
Talla

Da farko Dortmund ta kama hanyar ficewa gasar amma Ana mintinan karshe ne a kammala wasa ta samu nasarar jefa kwallo ta uku a raga ana ci 2-2, Sakamakon da bai yi wa Malaga dadi ba.

A daya bangaren kuma Real Madrid da ta lallasa Galatasaray ci 3-0 a karawa ta farko, amma a daren Talata ta sha kashi ne ci 3-2 a birnin Istanbul, amma kuma yaran Mourinho ne suka tsallake zuwa zagayen dab da na karshe da jimillar kwallaye ci 5-3.
Kocin Dortmund yace Allah ne ya dora su a sa’a bayan sun sha da kyar a hannun Malaga.

Mourinho ya yi jinjina ga kwazon da ‘Yan wasan Galatasaray suka nuna bayan doke shi a karawa ta biyu.

Emmanuel Eboue da Wesley Sneijder da Didier Drogba su ne suka jefawa Galatasaray kawallayenta a raga.

Cristiano Ronaldo ne kuma ya zirarawa Madrid kwallayenta biyu.

Wannan ne dai karo na bakwai da Mourinho ke tsallakewa zuwa zagayen dab da na karshe a matsayin koci a gasar zakarun Turai. Karo na uku ke nan Real Madrid na tsallakewa zuwa zagayen Dab dana karshe a jere.

A yau Laraba ne kuma za’a tantance sauran kungiyoyin biyu da za su bi sahun Real Madrid da kuma Dotmound, inda Barcelona za ta karbi bakuncin PSG, Juventus kuma ta fafata da Bayern Munich.

A karawa ta farko dai an tashi wasa ne ci 2-2 tsakanin Paris Saint-Germain da Barcelona. Kuma a yau Laraba PSG tana bukatar jefa kwallo daya kafin ta daidata da Barcelona.

Wata kafar yada labaran Faransa ta tambayi Mourinho shin ko wa zai goyi baya tsakanin PSG da Barcelona?

Sai dai Mourinho yace ai shi yana da abokai a Faransa amma baya da aboki a Barcelona, don haka zai so a yi waje da Barcelona.

Akwai dai alamun Barcelona za ta buga wasan ne ba tare da Messi ba wanda ke fama da rauni, amma kuma Andres Iniesta yace ko ba messi suna iya fita kunya

Bayern Munich kuma za ta kai wa Juventus ziyara ne tare da fatar kare nasarar da ta samu a karawa ta farko.

Kungiyar Bayern Munich tace a ranar 11 ga watan Mayu ne za ta yi bukin lashe kofinta na Bundesliga da ta lashe a bana aAllianz Arena.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.