Isa ga babban shafi
Wasanni

Harambe Stars na kokarin samun nasara a kan Eagles na Nigeria

Da alama mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Harambe star ta kasar Kenya, Adel Amrouche ya aiki ba kama hannun yaro, don ganin kungiyar tashi ta sami nasara, a wasan da za su buga da Nigeria, a ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya na shekera mai zuwa. Za dai a buga wannan wasan ne a ranar lahadi mai zuwa, wato 5 ga wannan watan na Mayu, birnin Nairobi, kuma zuwa yanzu kocin na ta sa ido kan ‘yan wasan kasar ta Kenya, da ke buga wasanni a kasashen waje, inda yace zai darje, ya zabi wadanda suke da karsashi, don ganin juya nasar da Nigeria ta samu a kan su a baya.Mataimakin kocin, James Nandwa, yace yanzu haka suna duba salon wasan ‘yan kasar fiye da 20, kuna akwai yiwuwar za a kira da dama daga cikin su. 

'Yan kungiyar Harambe Star, na kasar Kenya
'Yan kungiyar Harambe Star, na kasar Kenya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.