Isa ga babban shafi
Wimbledon

Wimbledon: Federer da Sharapova da Azarenka sun samu nasara a karawar farko

Zakaran Wimbledon Roger Federer ya fara farautar lashe kofin gasar karo na 8 bayan ya lashe wasan farko a karawar shi da Vicktor. Shekaru 10 ke nan da Roger Federer ya fara lashe kofin Wimbledon a Ingila. Victoria Azarenka ta Belerus mai rike da kofin US Open ta sha da kyar ne a karawar farko, Wacce ta buga wasan dab dana karshe a 2011 da 2012 a Wimbledon.

Roger Federer yana fafatawa a Wimbledon
Roger Federer yana fafatawa a Wimbledon Reuters
Talla

A wasan, sai da Azerenka ta barke da kuka saboda yadda ‘yar wasan rasha Maria Joa ta takura mata, inda har kafarta ta dama ta dare a lokacin da za ta buga kwallo.

A zagaye na biyu dai Azerenka zata kara ne da ‘Yar wasan Italia Flavia Pennetta.

Haka ma, Maria Sharapova ta tsallake zagaye na biyu bayan ta doke ‘Yar wasan Faransa Katrina.

Sara Eranni ta Italiya ta fuskanci bacin rana tun a zagayen farko bayan ta sha kashi a hannun matashiya Monica ‘yar kasar Puerto Rica.

Errani dai ta buga wasan dab da na karshe a Rolland Garros kuma ita ce ta buga wasan karshe da Maria Sharapova a bara.

A yau Linitini ne kuma Zakaran Rolland Garros Rafeal Nadal zai fara haskawa wanda ke neman huce hushhin bara a Wimbledon.

A bara Nadal ya fice ne saboda rauni, Kuma shi ne ya lashe kofin Rolland Garros sau 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.