Isa ga babban shafi
Premier League

City ta lallasa United, Arsenal ta dare Tebur

Manchester City ta lallasa Manchester United ci 4-1 a premier league ta Ingila, Karawa ta farko da David Moyes ya sha kashi a hannun abokiyar hamayyar Manchester United. Sergio Aguero ne ya jefa kwallaye biyu a raga sai kuma Yaya Toure da Samir Nasri da suka jefa sauran kwallayen a ragar Manchester United.

Sergio Aguero na Manchester City wanda ya jefa kwallaye biyu a ragar Manchester United
Sergio Aguero na Manchester City wanda ya jefa kwallaye biyu a ragar Manchester United REUTERS/Phil Noble
Talla

Kungiyar Arsenal ce yanzu ke jagorancin teburin Premier da maki 12 bayan ta lallasa Stoke ci 3-1. Kwallayen da Ozil ya mika aka zira a raga.

Tottenham ce a matsayi na biyu da maki 12, yayin da City da Chelsea da Liverpool ke matsayi na uku da hudu da Biyar, dukkaninsu da maki 10.

Kungiyar Sunderland kuma ta sallami kocinta, Paolo Di Canio bayan kungiyar ta sha kashi ci 3-0 a hannun West Brom, Kuma Sunderland ce a kasan teburin Premier da maki guda kacal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.