Ba zan yi saurin sabunta kwantiraki na da Arsenal ba – Wenger
Mai horar da ‘yan wasan kungiyar Arsenal a gasar Premier, Arsene Wenger, ya ce ba zai yi hanzarin sabunta kwantirakinshi da kungiyar ba.
Wallafawa ranar:
Dan shekaru 64, Wenger ya kasance cikin kakar wasa ta karshe a kwantirakinshi da Arsenal wacce hukumominta ke nunawa suna bukatar ya ci gaba da kasancewa da su.
Sai dai Wenger ya ce wannan ba lokacin da za a tsaya ana magana a kan kwantiraki bane domin yana so ya mayar da hankalinshi akan bunkasa kungiyar.
Tun a shekarar 1996 Wenger ya karbi ragamar kungiyar shine kuma koci da ya dade yana jagorantar kungiyar ta Arsenal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu