Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Kocin Jamus ya sabunta kwantirakinshi

Mai horar da ‘yan wasan Jamus Joachim Loew ya sabunta kwantirakinshi wanda zai kai shi har tsawon shekarar 2016 a cewar hukumar kwallon kafar kasar (DBF) ta bayyana a yau Juma’a.

Mai horar da 'yan wasan Jamus, Joachim Loew
Mai horar da 'yan wasan Jamus, Joachim Loew topnews.in
Talla

Kwantirakin Leow ya kamata ya kare ne a shekarar 2014, wato har bayan gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil, amma Shugaban hukumar DBF, Wolfgang Niersbach ya nemi Leow da ya sabunta kwantirakinshi zuwa 2016.

A cewar Niersbach tun daga shekarar 2006 kasar Jamus na karewa ne a rukunin kasashen hudu a gasar ta cin kofin duniya da kuma na nahiyar Turai sannan sun samu damar shiga gasar ta badi.

“Duk wannan kokarin Leow ne da tawagarshi saboda haka hukumar DBF na so ta nuna yardarta da jagorancinshi.” Inji Niersbach.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.