Isa ga babban shafi
Champions League

Lewandowski zai fice Dortmund a badi

Dan kasar Poland Robert Lewandowski ya tabbatar da kudirin ficewa kungiyar Borussia Dortmund a karshen kakar bana. Dan wasan yace zai fice ne domin kwadayin wata rayuwa a wata sabuwar kungiya.

Robert Lewandowski, Dan wasan Borussia Dortmund, wanda ya jefa kwallaye 4 a ragar Real Madrid a gasar zakarun Turai a bara
Robert Lewandowski, Dan wasan Borussia Dortmund, wanda ya jefa kwallaye 4 a ragar Real Madrid a gasar zakarun Turai a bara REUTERS/Ina Fassbender
Talla

Bayan ya dade yana wa kungiyar barazanar ficewa, A yau Laraba, Lewandowski yace zai fice ne a badi idan har kwangilar shi da Dortmund ta kawo karshe a watan Yuni.

Dan wasan yace yana dab da bayyana kungiyar da zai dosa anan gaba, amma tuni aka ruwaito dan wasan yana son komawa ne Bayern Munich, da ke adawa da Dortmund a Bundesliga.

Gasar Zakarun Turai

A yau Laraba akwai ci gaba da gasar zakarun Turai Kuma Lawandowski zai haska a wasan da Arsenal zata kara da Borussia Dortmund. Kungiyar Chelsea ta Ingila kuma zata karbi bakuncin Schalke 04 ce ta Jamus.

Atletico Madrid kuma zata iya tsallakewa zuwa zagaye na biyu idan har ta doke Austria Vienna.

Akwai wasa tsakanin Barcelona da AC Milan a filin wasa Nou Camp. Kuma a yau ido zai dawo ne ga Messi wanda ya buga wasanni hudu ba tare da ya zira kwallo a raga ba.

Tun dawowarsa daga jinyar rauni, Barcelona ta buga kwallo da Osasuna da Real Madrid da Celta Vigo da kuma Espanyol ba tare da Messi ya kada kwallo a raga ba. Wanda cikin shekaru biyu shi ne lokaci mai tsawo da dan wasan ya kwashe yana yunwar kwallo a raga.

Kungiyar Celtic kuma zata fafata ne da Ajax a Amsterdam

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.