Isa ga babban shafi
Bundesliga

Lewandowski zai fice Dortmund

Robert Lewandowski wanda ya jefa dukkanin kwallaye 4 a ragar Madrid a gasar zakarun Turai zagayen dab da na karshe karawar farko, wakilin shi yace dan wasan zai fice daga Borussia Dortmund domin ya amince ya kulla yarjejeniya da wata Kungiya.

Robert Lewandowski, Dan wasan Borussia Dortmund, wanda ya jefa kwallaye 4 a ragar Real Madrid a gasar zakarun Turai
Robert Lewandowski, Dan wasan Borussia Dortmund, wanda ya jefa kwallaye 4 a ragar Real Madrid a gasar zakarun Turai Reuters
Talla

Robert Lewandowski  ya nuna wa duniya kansa a gasar zakarun Turai, wanda ke kokarin taimakawa Dortmund kai ziyara filin wasa naWembley a wasan karshe idan dan wasan ya maimaita barnar da ya aikatawa Madrid a Santiago.

Rahotanni dai masu karo da juna na kawarmata cewa Lewandowski zai koma taka kwallo ne a Bayern Munich ko Manchester United, yayin da wasu rahotanni kuma ke cewa dan wasan zai koma taka kwallo ne a Juventus.

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya amsa shan kashi yana mai cewa Borussia Dortmund sun cancanci nasarar da suka samu saboda yadda suka taka kwallo.

Sai dai kuma Mourinho yace komi na iya faruwa a karawa ta biyu. Saboda kwallon da Ronaldo ya zira a gidan Dortmund.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.