Isa ga babban shafi
Champions League

Sai Sa'a mu rama kashin da muka sha, inji Messi

Dan wasan Barcelona kuma zakaran duniya Lionel Messi ya amsa sun sha kashi a hannun Bayern Munich a gasar zakarun Turai zagayen dab dana karshe. Bayern ta lallasa Barca ne ci 4-0 a karawa ta farko.

Lionel Messi da Xavi na Barcelona a lokacin da suka sha kashi a hannun Bayern Munich.
Lionel Messi da Xavi na Barcelona a lokacin da suka sha kashi a hannun Bayern Munich. Reuters
Talla

Wannan labarin ya ja hankalin jaridun wasanni a kasashen duniya musamman a Spain.

Jaridar adawa ta Marca a birnin Madrid ta wallafa babban labarinta ne mai taken “Ranar da babu irinta”, Jaridar Mundo Deportivo kuma a Barcelona ta wallafa labarinta ne mai taken “Annoba ta shafi Barcelona.

Kwallaye hudu da Bayern Munich ta zira a ragar Barcelona ya kare wa ‘Yan wasan Barca kwarin gwiwa bayan an tambaye su ko suna iya mayar da martani a karawa ta Biyu.

“Sun fi karfinmu, mun sha kashi domin sun fi mu ta ko ina” inji Messi.

Messi yace abu ne me wahala su rama kashin da suka sha a karawa ta biyu da za’a gudanar a ranar Laraba a Nou Camp.

A karshen Makon nan Barcelona na iya lashe kofin La liga idan sun doke Athletic Bilbao a ranar Assabar, amma sai idan Real Madrid ta sha kashi a hannun Atletico Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.