Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta tsawaita lokacin zaben gwarzon Dan wasan duniya

Hukumar FIFA da ke kula da kwallon kafa a duniya ta tsawaita lokacin jefa kuri’ar zaben gwarzon dan wasa a bana har zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba bayan da wa’adin da hukumar ta diba ya kawo karshe ba tare da samun wadatattun kuri’u ba.

Cristiano Ronaldo wanda ya taimakwa Portugal tsallakewa zuwa Brazil a badi bayan ya jefa kwallaye uku a ragar Sweden.
Cristiano Ronaldo wanda ya taimakwa Portugal tsallakewa zuwa Brazil a badi bayan ya jefa kwallaye uku a ragar Sweden. AFP
Talla

Tun a ranar Juma’ar makon jiya ne wa’adin kammala kada kuri’ar ya kawo karshe amma a makon nan za’a ci gaba da jefa kuri’a wanda hakan ake ganin zai iya taimakawa Cristiano Ronaldo lashe kyautar musamman ruwan kwallaye da ya yi a ragar Sweden wanda ya ba Portugal damar tsallakewa zuwa gasar cin kofin Duniya a Brazil.

Yanzu dai Ronaldo da Ribery ne a sahun gaba da ake hasashen za su iya lashe kyautar sabanin Messi wanda yanzu haka ke jinya.

Ribery yana cikin tawagar ‘Yan wasan da suka taimakawa Faransa tsallakewa zuwa Brazil bayan ya lashe kofuna uku a Bayern Munich a kakar da ta gabata.

Ribery ne ya doke Ronaldo da Messi a takarar gwarzon dan wasan Turai.

A ranar 13 ga watan Janairun badi ne za’a bayyana sunan wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a bana a birnin Zurich. Sai dai kuma Ronaldo yace zai kauracewa halartar bukin da za’a gudanar ko da shi ne ya lashe kyautar a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.