Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Dortmund za ta karbi bakuncin Bayern Munich

Hankali zai koma a Bundesliga ta Jamus inda Borussia Dortmund za ta karbi bakuncin Bayern Munich a gobe Assabar, kungiyoyin masu hamayya da juna wadanda ke jagorancin teburin gasar.

Kocin kungiyar Bayern Munich Pep Guardiola
Kocin kungiyar Bayern Munich Pep Guardiola REUTERS/Michael Dalder
Talla

Borussia Dortmund da Bayern Munich ne suka buga wasan karshe a gasar Zakarun Turai inda ake danganta karawar kungiyoyin biyu tamkar kamar Clasico a Spain tsakanin Barcelona da Real Madrid.

Bayern Munich ce ke jagorancin teburin gasar da tazarar maki 4 tsakaninta da Dortmund. Amma dukkanin kungiyoyin biyu suna fama da matsala, domin mafi yawancin manyan ‘yan wasansu suna jinya.

Bayern Munich za ta buga wasan ne ba tare da Ribery ba wanda ya samu rauni a karawa tsakanin Faransa da Ukraine.

Bayern Munich dai ta doke Dortmund a wasan karshe a gasar zakarun Turai, wanda ya ba kungiyar damar lashe kofuna uku a kakar da ta gabata amma tun shekarar 2010 rabon da Bayern Munich ta doke Dortmund a Bundesliga.

Sai dai kuma a bana Bayern Munich ta buga wasanni 37 ba tare da samun galabarta karkashin jagorancin Pep Guardiola.

Spain

A La liga Barcelona za ta karbi bakuncin Granada ne a gobe Assabar sai dai akwai zubin ‘yan wasa kusan guda 7 da ke jinya a tawagar Barcelona kuma babban limamen majinyatan shi ne Messi wanda Barcelona za ta kwashe makwanni 6 ba tare da shi ba.

Akwai kuma mai tsaron gidan Barcelona Victor Valdes wanda ya samu rauni a wasan da Spain ta sha kashi ci 1-0 a hannun Afrika ta Kudu.

Sannan akwai Dani Alves da kungiyar tace zai kwashe kawanki 10 yana jinya sai kuma Gerard Pique da Cesc Fabregas da Xavi Hernandez wadanda babu tabbas ko suna iya buga wasan.

Barcleona dai zata dogara ne da Neymar a madadin Messi, yayin da kuma Real Madrid zata kara da Almeria tare da fatar datse tazarar maki da ke tsakaninta da Barcelona.

Atletico Madrid da ke a matsayi na biyu a teburin gasar za ta karbi bakuncin Getafe ne a gobe Assabar.

Ingila

A Premier league Arsenal da ke jagorancin teburin gasar za ta kara ne da Southampton a gobe Assabar yayin da Liverpool da ke bi mata a Tebur zata kara da Everton. Chelsea kuma zata kece raini da West Ham.

A ranar Lahadi ne Manchester United zata kara da Cardiff a karon farko tun 1974. Akwai wasan kece raini tsakanin Manchester City da tottenham.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.