FIFA
Bayern Munich ta lashe kofin Duniya a Morocco
Kungiyar Bayern Munich ta lashe kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa na duniya bayan ta doke kungiyar da ta wakilci Afrika Raja Casablanca ta Morroco ci 2-0. Wannan ne kofi na Biyar da Bayern Munich ta lashe a 2013 bayan lashe kofin Super na Turai da kofin zakarun Turai da Bundesliga da kofin Jamus.
Wallafawa ranar:
Talla
Wannan ne kuma karo na uku da Pep Guardiola ya lashe kofin gasar bayan ya lashe kofin sau biyu a lokacin da yana Barcelona.
Wadannan kofunan da Bayern Munich ta lashe Franck Ribery yana fatar zai doke Messi da Ronaldo domin zama gwarzon duniya a bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu