Isa ga babban shafi
CAF

Mikel da Yaya Toure da Drogba ke takarar gwarzon Afrika a bana

Hukumar da ke kula da sha'anin Kwallon kafa a Afrika CAF ta ware sunan John Obi Mikel na Najeriya da Yaya Toure da Didier Drogba na Cote d'Ivoire a matsayin wadanda za'a zabi Gwarzon Afrika a bana.

Yaya Toure na Manchester City da Didier Drogba, na Galatasaray da John Obi Mikel na Chelsea wadanda ke takarar gwarzon Afrika a bana
Yaya Toure na Manchester City da Didier Drogba, na Galatasaray da John Obi Mikel na Chelsea wadanda ke takarar gwarzon Afrika a bana Mediafax Foto/AFP
Talla

Yaya Toure mai shekaru 30 da ke taka kwallo a Kungiyar Manchester City yana neman lashe kyautar ne karo na uku a jere, bayan ya lashe kyautar a 2011 da 2012.

Didier Drogba, ma da ke taka leda a kungiyar Galatasaray ta Turkiya, ya taba lashe kyautar har sau biyu a shekarar 2006 da 2009.

Wannan ne kuma karon farko da aka zabi Mikel Obi cikin ‘yan wasa uku da za’a zaba gwarzon Afrika. Inda wasu masoya kwallon kafa a Afrika ke ganin ya dace ace Dan Najeriya ya lashe kyautar a bana saboda John Mikel Obi ne ya jagorancin tawagar Super Eagle da suka lashe kofin Afrika a kasar Afrika ta Kudu.

A ranar 9 ga watan Janairu ne za’a bayyana sunan wanda ya lashe kyautar gwarzon na Afrika a birnin Lagos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.