Isa ga babban shafi
CAF

CHAN 2014: Ghana da Libya zasu yi fafatawar karshe

Kasar Ghana da Libya su ne zasu fafata a wasan karshe bayan sun samu nasara a jiya Laraba a wasannin kasashen Afrika da a ke gudanarwa a kasar Afrika ta Kudu. ‘Yan wasan Black Stars na Ghana sun doke ‘Yan wasan Super Eagles ne na Najeriya ci 4-1 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a zagayen dab dana karshe.

Ghana ta tsallake zuwa guda wasan karshe bayan ta doke Najeriya ci 4-1 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a gasar kasashen Afrika da ake gudanarwa a kasar Afrika ta kudu.
Ghana ta tsallake zuwa guda wasan karshe bayan ta doke Najeriya ci 4-1 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a gasar kasashen Afrika da ake gudanarwa a kasar Afrika ta kudu. CAF
Talla

Kasar Ghana za ta yi fatar lashe kofin a bana domin huce hucin kofin da ta rasa a shekarar 2009 a karawarta da Congo.

Kasar Libya ta tsallake ne bayan ta doke Zimbabwe ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida

Duk kungiyar ta lashe kofin gasar zata kwashi kudi dala 750,000, mai bi ma ta zata karbi kudi dala 400,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.