Isa ga babban shafi
La liga

Atletico ta sake yin bari

Sai a karshen mako mai zuwa ne za’a yi ta kare tsakanin Atletico Madrid da Barcelona bayan kungiyoyin biyu sun yi barin maki a jiya Lahadi. Atletico ta yi kunnen doki ci 1 da 1 da Malaga wanda sakamakon wasan ya jinkirtawa wa Kungiyar lashe kofin La Liga a karon farko tsawon shekaru 18 bayan kungiyar Elche ta rike Barcelona babu ci a raga.

Dan wasan Atletico Madrid Koke yana juyayi bayan ya barar da kwallo a raga
Dan wasan Atletico Madrid Koke yana juyayi bayan ya barar da kwallo a raga REUTERS/Sergio Perez
Talla

Sai a ranar Assabar ne kungiyoyin biyu zasu fafata da juna, amma idan har Barcelona zata lashe kofin dole sai ta doke Atletico yayin da kuma idan an tashi babu ci ko kunnen doki Atletico Madrid ce ta lashe kofin.

Yanzu an yi waje da Real Madrid a hamayyar lashe La liga bayan ta sake shan kashi ci 2-0 a hannun Celta Vigo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.