Isa ga babban shafi
Wasanni

Kyaututukan da aka bayar a gasar Kofin Duniya a Brazil

Bayan cin daya mai ban haushi da Jamus ta yi wa Argentina a wasan karshe na cin kofin duniya da aka yi a dare Lahadi, ba wai kawai hana wa Argentimna daukar kofin da aka kera da zinare samfurin 18 Carat ba ne, hakan kuma ya haramta wa kasar karbar kudi Dalar Amurka miliyon 35.

Daruruwan magoya bayan Jamus suna murnar doke Faransa a gasar cin kofin duniya a Brazil
Daruruwan magoya bayan Jamus suna murnar doke Faransa a gasar cin kofin duniya a Brazil REUTERS/Steffi Loos
Talla

Wannan ne tukuici mafi girma da aka taba yi a gasar ta cin kofin duniya, don ko Spain da ta lashe gasar a shekarar 2010, Dala miliyon 30 ne ta karba.

Wanann kudin shi ne kawai zai zama halaliyar kasar ta Jamus, don kuwa hukumar ta FIFA za ta karbe kofin na asali, sannan a bai Jamus wani irinshi amma mai wanda kimarsa ba ta kai wannan ba kamar dai yadda aka saba.

Sauran Kyaututuka

To ko baya ga kasar Jamus da ta dauki kofin, su ma sauran kasashe da suka shiga gasar an ba su tukuci daban daban;
Kasar Argentina da ta zo ta 2 ta samu dala miliyan $25, da an bayar da $24 million ne a shekara ta 2010.
Netherlands wadda ta zo ta 3 ta samu $20 milyan.
Brazil ta 4 a wannnan gasa ta bana ta samu $18 million.

Sauran Kasashe

Kasashen da suka kai zagayen ‘yan 16 sun karbi Dalar Amurka miliyann $9.
To sai dai za a mika wadannan kudade ne ga hukumomin kwallon kafa na kasashensu ba wai kai-tsaye a hannun ‘yan wasa ko kuma kociya ba.
Kafin a fara wasan kuma, ana bai wa kowacce kasa Dala Miliyan 1 da rabi don horaswa da kuma tafiye tafiyen ‘yan wasa.

FIFA ta kuma ware wasu kudaden dala miliyon 70, da za a biya kulob kulob din da suka tafi gasar, inda za a biya kowane kulob dala dubu 2 da 800 kan kowane dan wasa.

Tukuicin Brazil Mai Masaukin Baki

Kasan Brazil da ta yi hidimar daukar nauyin gasar za ta karbi wasu kudadem amma ba a san yawansu ba zuwa yanzu, don FIFA ba ta gama harhada irin ribar da ta samu ba, sai dai fa kudin da Brazil za ta samu ba za su kai Dala Biliyo 14 da kasar ta kashe wajen shirya wannan gasa ba.

FIFA Ta Ci Gagarumar Riba

Watakila jama’a za su iya cewa hukumar ta FIFA ta kashe makuddan kudade a wannan batu, to sai dai idan aka yi la’akari da irin kudaden da take samu daga shirya wannan gasa, wannan bai taka kara ya karya ba.
A jimilce dai FIFA ta samu kudaden da yawansu ya haura dala bilyan 4 da milyan 500 a bana, kuma ta same su ne daga lasisin da kafafen yada labarai suka biyo domin samun izinin nuna gasar, da kudaden tallace-tallace da dai sauransu.

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.