Isa ga babban shafi
Tennis

Tsonga ya doke Djokovic a Toronto

Jamurumin Tennis na Duniya Novak Djokovic wanda bai dade da yin aure ba ya sha kashi a hannun Jo-Wilfried Tsonga na Faransa a gasar Toronto Masters zagaye na uku. Roger Federer kuma ya tsallake zuwa zagaye na gaba bayan ya doke dan wasan Croatia Marin Cilic.

Novak Djokovic na Serbia
Novak Djokovic na Serbia REUTERS/Suzanne Plunkett
Talla

A yau Juma’a ne Federer ke bikin ranar haifuwarsa inda ya ke cika shekaru 33.

Bangaren Mata

A gasar Montreal bangaren mata an yi waje da Jaruman Tennis na duniya inda Petra Kvitova da ta lashe Wimbledon da Maria Sharapova da ta lashe Rollad Garros suka sha kashi a gasar.

Ekaterina Makarova ta Rasha ita ce ta yi waje da Kvitova, yayin da kuma Carla Suarez ta doke Sharapova. Serena Williams kuma ta tsallake ne zuwa kwata fainal bayan ta doke Lucie Safarova.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.