Isa ga babban shafi
La liga

Za’a soma La liga

A kaka da ta gabata Atletico Madrid ce ta ratso tsakanin Barcelona da Real Madrid ta lashe kofin La liga karon na farko tsawon shekaru 18 tana farautar kofin. A bana ma Atletico Madrid zata bayar da mamaki da sabbin ‘yan wasan da yo cefane bayan ta sayar da wasu manyan ‘Yan wasanta da suka lashe mata kofin La liga, irin su Diego Costa.

Fafatawar Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid a La liga
Fafatawar Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid a La liga Reuters
Talla

Saboda wasan Super Cup a yau Juma’a, Sai a ranar Litinin ne Atletico Madrid zata fara kece raini da Rayo Vallecano. Real Madrid ma sai a ranar litinin zata karbi bakuncin Cordoba.

Kungiyar Barcelona da ba ta lashe kofi ba a kaka da ta gabata za ta fara karawa ne da Elche a ranar Lahadi . A karon farko kuma Luis Enrique zai jagoranci kungiyar a La liga bayan ya gaji Gerardo Martino da ya kasa lashe wa Barcelona kofi.

Barcelona zata fara La liga ne ba tare da wasu sabbin ‘Yan wasan da ta sayo ba, Marc-Andre ter Stegen da Thomas Vermaelen da ke fama da rauni, da kuma Luis Suarez da aka haramtawa wasanni na wata hudu saboda ya ciji Giorgio Chiellini na Italiya a gasar cin kofin duniya a Brazil

A gobe Assabar akwai wasanni kamar haka:

Malaga v Athletic Bilbao

Sevilla v Valencia

Granada v Deportivo la Coruna

Almeria v Espanyol

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.