Faransa ta doke Spain
Kasar Faransa ta doke Spain ci 1 da 0 a Paris, kuma Loic Remy ne ya jefawa Faransawa kwallo a ragar Spain bayan dawo wa hutun rabin lokaci. Kodayake a wasan Spain ta yi amfani ne da matasa, domin duka Santi Cazorla ne tsoho a cikin wasan, bayan Xavi Hernandez da Alonso sun yi ritaya.
Wallafawa ranar:
Sakamakon Wasannin zumunci
Italiya 2 Netherlands 0
Belarus 6 Tadjikistan 1
Croatia 2 Cyprus 0
Sweden 2 Estonia 0
Tarihi
Zlatan Ibrahimovic ya kafa tarihi a matsayin wanda ya fi kowa zira kwallaye a raga a tarihin kasar Sweden bayan ya zirara kwallon shi ta 50 a haskawa 99 da ya yi wa kasarshi a jiya Alhamis da suka doke Estonia.
A ranaar Litinin ne zai yi haskawa ta 100 a karawar da Sweden za ta yi da Austria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu