Kotu ta ce Oscar Pistorius bai aikata kisan Budurwarsa da gangan ba
Alkalin Kotun da ke sauraron karar da aka shigar da tsohon dan tseren nakasassun nan wato Oscar Pistorius a kasar Afruka ta kudu Thokozile Masipa ta yanke hukuncin cewar Kotu bata samu Oscar Pistorius da laifin aikata kisan Reeva Steenkamp da gangan ba
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Alkalin ta ce, binciken da aka yi bai bayyanawa Kotun cewar an samu Pistorius dumu-dumu da laifin aikata kisan ba, sai dai Kotu ta lura da cewar Pistorius cikin hayyacinsa ya dauki Bindiga ya kuma yi harbi, amma ba da niyyar kisan Budurwarsa ba.
A bisa wannan dalilin inji Alkali Masipa Kotu bata samu Oscar da laifin kisan Reeva da gangan ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu