An hada Afrika ta kudu a rukuni mai zafi
An hada rukunin kasashen da zasu fafata a gasar cin kofin Afrika da za’a gudanar a kasar Equatorial Guinea, kuma a rukunin A an hada Equatorial Guinea mai masaukin baki rukuni guda da Gabon da suka taba karbar bakuncin gasar a 2012 da kuma Congo da Burkina Faso.
Wallafawa ranar:
Rukunin B kuma an hada Zambia ne da Jamhuriyyar Congo da Cape Verde da kuma Tunisia.
Rukunin C wanda ake ganin ya fi zafi da jan hankali, an hada kasar Afrika ta kudu ne da Ghana da Senegal da kuma Algeria.
A rukunin D an hada Cote d’Ivoire ne da Guinea da Kamaru da kuma Mali
A ranar 17 ga watan Janairu ne za’a fara gasar a kammala 8 ga watan Fabrairun 2015.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu