Isa ga babban shafi
CAN 2015

CAF ta yaba da shirin Equatorial Guinea

Hukumar CAF da ke kula da sha’anin kwallon kafa a nahiyar Afrika tace ta gamsu da shirin kasar Equatorial Guinea na karbar bakuncin gasar cin kofin Nahiyar da za a fara a ranar Assabar duk da cewa wasu kasashe na korafi akan wasu filayen wasanni da za a buga wasan.

Filayen wasanni a kasar Equatorial Guinea
Filayen wasanni a kasar Equatorial Guinea
Talla

CAF tace ta gamsu da filayen wasannin a garuruwan Mongomo da Ebebiyin kamar yadda sakataren hukumar Hicham El Amrani ya shaidawa manema labarai a birnin Bata.

Za a dai gudanar da wasannin ne a biranen Bata da Malobo da kuma garuruwan Mongomo da Ebebiyin.

Cikin watanni biyu ne Equatorial Guinea ta shirya karbar bakuncin gasar bayan Morroco ta janye saboda tsoron cutar Ebola.

Masu shirya gudanar da wasannin na Afrika sun ce za su sayar da tikitin shiga kallon wasannin cikin rahusa inda suka ce za su caji kudi kasa da dala.

Tuni kuma shugaban kasar Equatorial Guinea yace zai yi sadaqar tikicin shiga kallon wasannin guda 40,000

Equatorial Guinea za ta fara fafatawa da Congo Brazzaville a rukuninsu na Farko. Daga bisani ne kuma Gabon ta fafata da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.