Isa ga babban shafi
CAN 2015

CAF ta dakatar da alkalin wasan Mauritania

Hukumar kwallon Afrika CAF ta dakatar da wani alkalin wasa dan kasar Mauritania Rajindraparsad Seechurn har na tsawon watanni 6 tare da cin kasar Tunisia tarar kudi dala dubu hamsin, sakamakon abin da ya faru a wasan kwata fainal da Equatoria Guinea ta yi waje da Tunisia a filin wasa na garin Bata.

Shugaban kwallon Afrika Issa Hayatou.
Shugaban kwallon Afrika Issa Hayatou. AFP PHOTO / FADEL SENNA
Talla

Ana dab da kammala wasa ne alkalin wasa ya ba Equatorial Guinea fanariti bayan Tunisia ta fara jefa kwallo a raga.

Bayan an kara lokaci kuma Equatorial Guinea ta sake jefa kwallo a ragar Tunisia inda suka tashi ci 2-1 a ranar Assabar.

Amma a lokacin da kyar alkalin wasa ya sha a hannun ‘yan wasan Tunisia, har sai da ‘yan sanda suka raka shi.

A cikin sanarwar da CAF ta fitar ta kuma bayyana cewa ta ci tarar Equatorial Guinea kudi dala dubu biyar, saboda magoya bayanta da suka shiga filin wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.