Isa ga babban shafi
Argentina

Messi ya sha suka a Argentina

Rahotanni daga Argentina na cewa Messi zai dauki hutu na dan wani lokaci daga bugawa kasar shi kwallo domin jimamin rashin lashewa Argentina kofi bayan Chile ta doke su a Copa America.

Lionel Messi na Argentina
Lionel Messi na Argentina AFP PHOTO / PABLO PORCIUNCULA
Talla

Jaridun Argetina sun sharhanta cewa saboda suka da Messi ke fuskatanta daga ‘yan kasar Argentina zai sa Dan wasan ya tafi hutu na wani lokaci.

Jaridar wasanni ta Ole tace Messi ya fuskanci suka daga ‘Yan Argentina, inda wasu ke cewa ya fi kaunar Barcleona kungiyar da ya lashe kofuna da dama fiye da kasar shi.

Jaridun Spain sun ruwaito cewa Messi ya ki amincewa da kyautar gwarzon dan wasa a gasar Copa America da aka kammala a karshen makon da ya gabata.

Sau biyu ana doke Argentina da Messi a wasan karshe a Copa America inda Chile ta doke su 4 da 1 a bugun fanariti a wasan karshe a bana da kuma 2007 lokacin da Brazil ta doke su Messi 3-0 a wasan karshe.

Sannan Messi ya sha kashi a hannun Jamus a gasar cin kofin duniya wasan karshe da suka fafata a Brazil.

Wasu na ganin har yanzu Messi bai yi darajar Maradona ba a Argentina wanda ya lashe wa kasar kofin duniya a 1986.

Sai dai kuma Messi ya fi Maradona yawan zirara kwallaye a raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.